Yan gudun hijira dake wajen Najeriya ba za su yi zabe ba -INEC


Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ce ba gaskiya bane rahotannin dake cewa tayi wani shiri na musamman da zai bawa yan gudun hijira dake wajen kasarnan damar yin zabe.

A wata sanarwa kwamishinan wayar da kan masu kada kuri’a da sadarwa na hukumar ya ce yan kasar waje baza su yi zabe ba a shekarar 2019.

Sanarwar ta ce yan gudun hijira da yanzu suke zaune ba a jihar da suka yi rijista ba, to za suyi zaben shugaban kasa ne kawai.

Jam’iyar adawa ta PDP dai tayi zargin cewa hukumar zaben na shirin tafka magudi a zaben shekarar 2019 ta hanyar bude wasu tashoshin zabe , a makotan kasashe.

Jam’iyar ta ce hukumar za ta bude tashoshin zaben ne a kasashen Kamaru da kuma Nijar.


Like it? Share with your friends!

-2
79 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like