Yan Fashi sunyi Dirar Mikiya A Wani Kauye Dake Jihar Kaduna Inda Sukayi Awon Gaba Da Shanu Masu Yawa


Yan fashi da makami masu yawan gaske ne suka mamaye Kungi wani gari dake da tazarar kilomita 8 daga garin Birnin Gwari inda sukayi awon gaba da duk wani garken shanu da idonsu yayi arba dasu. 

  Wani mazaunin garin Alhaji Saidu Kungi, ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewa  yan bindigar sun isa kauyen da karfe 11 daren Litinin inda suka haifar da rudani ta hanyar harbi ta ko’ina.

Yace yan fashin sun rika bi gida-gida tare da umartar wadanda suka ajiye shanu da su bude inda suke  daga nan suka rika kora shanun cikin daji tare da tsorata mutane ta hanyar harbi har sai da suka gama fashin da misalin karfe 2 biyun dare. 

 Kungi yace motar yan sanda ta iso garin sanadiyar harbe-harben da suka ji  bayan da yan fashin suka tafi inda suka nemi mazauna garin dasu nuna musu hanyar da  suka bi. 

Yace lokacin da yan sandan suka yi yinkurin binsu sai suka juyo suna harbi hakan yasa yan sandan suka ja da baya. 

Kimanin shanu 38 yan fashin suka kwace a garin kuma har kawo yanzu ba  a gano ko daya ba aciki.

Comments 0

Your email address will not be published.

Yan Fashi sunyi Dirar Mikiya A Wani Kauye Dake Jihar Kaduna Inda Sukayi Awon Gaba Da Shanu Masu Yawa

log in

reset password

Back to
log in