Yan fashi sun kashe yan sanda 8 a jihar Kogi


Mutane 9 aka kashe ciki har da yan sanda 8 a garin Isanlu dake jihar Kogi lokacin da wasu gungun yan fashi da makami suka kai farmaki reshen daya daga cikin manyan bankunan kasuwanci da ake da su a kasarnan.

Baturen yan sandan na yankin (DPO) na daga cikin yan sandan da aka kashe a harin.

Baturen yan sandan da wasu yan sanda mata su biyu da kuma yan sanda hudu an kashe su ne a cikin ofishin yan sandan sai kuma jami’in dan sanda guda da aka kashe shi a harabar bankin.

Daya mutumin wanda farar hula ne ya mutu ne sakamakon harsashi da ya same shi.

Yan fashin dauke da bindigogi sun fara farma ofishin yan sandan inda suka saki dukkanin mutanen da suke a tsare kafin su kashe yan sandan.

Daga bisani ne suka isa bankin inda suka kwashe wasu makudan kudade da ba a san yawansu ba.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like