‘Yan Fashi Sun Kashe Sama Da Mutane 20 A Jihar Sokoto


Wasu ‘yan ta’adda sun hallaka sama da mutane 20 a kauyen Dan Tatsako na karamar hukumar Goronyo, jihar Sokoto.

Wata majiya a karamar hukumar ta ce ‘yan ta’addan sun je kauyen a cikin dare dauke da manyan makamai, inda suka fara harbi na kan mai uwa da wabi.

Majiyar ta ce bayan mutane 20 din da aka kashe, ‘yan fashin sun salwantar da gidaje da sauran kayayyakin al’ummar kauyen.

Ta kara da fadin cewa sauran mutanen kauyen sun gudu daga kauyen zuwa kauyukan kusa da su da ke kananan hukumomin Goronyo da Isa domin neman mafaka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, Muhammad Saddik, ya bayar da tabbacin afkuwar farmakin.


Like it? Share with your friends!

2

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like