Yan Fashi Da Makami Sun Kashe Wani Kaftin Na Soja, Da Kuma Wasu Mutane 3, A Kaduna  


Mutane hudu, da suka hada da wani babban soja mai mukamin Kaftin, da kuma jariri na daga cikin wadanda yan fashi da makami suka kashe akan hanyar Kaduna Zuwa Birnin Gwari.

Daya daga cikin wadanda suka tsira da ransu wanda maaikacin hukumar Kwastam ne yace lamarin yafaru ne lokacin da suka bar Kaduna da misalin karfe 8:00 na safe kuma sun nufin Ilorin babban birnin jihar Kwara cikin jerin gwanon motoci uku mallakar kamfanin sufuri na Kwara Express kawai sai sukaci karo da yan fashin su kimanin 20 a dai-dai  garin Palwaya dake karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna da misalin karfe 10:30 na safe.

Yace yan fashin sun tsayar dasu amma direban motar yayi kokarin guduwa, su kuma suka bude wuta kan motar inda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutanen.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Kaduna,ASP Moukhtar Husseini Aliyu yace bayanan da suka samu sun nuna cewa mutane uku ne suka mutu a lamarin.

Yace rundunar na cigaba da bincike dan ganin an kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki. 

 

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like