Yan Boko Haram sun kai hari garin Damboa


Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin Damboa dake jihar Borno.

Mazauna garin sun bayyana cewa mayakan kungiyar masu yawan gaske sun kaddamar da hari kan garin da misalin karfe 06:30 na safiyar ranar Laraba inda suka rika harbin kan me uwa da wabi.

Daya daga cikin mazauna garin ya bayyana cewa sojojin birged ta 25 dake garin Damboa sun shafe sama da sa’a guda suna musayar wuta da yan ta’addar.

“Sun zo a motoci masu yawa kirar Hilux. Munga kusan guda ashirin kafin mu fara gudu cikin daji,” daya daga cikin yan garin ya fadawa jaridar The Cable.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari garin Bwalakila dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like