Yan bindinga sun sace mutane shida a Adamawa


Barayi dauke da makamai sun sace wasu mutane shida daga wani kauye dake kan iyaka a jihar Adamawa.

Mazauna kauyen sun bayyana cewa gungun yan bindiga sun dira kauyen Gurin a karamar hukumar Fufore dake kan iyakar Najeriya da Kamaru inda suka sace wasu matasa shida.

“Matasa shida dake kiwon shanu aka sace da karfin bindiga tare da awon gaba da su ya yin da aka kyale shanunsu suna watangaririya,” ya ce.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa,Sulaiman Nguroje ya ce maharan sun sace mutane uku daga kauyen.

“Mutane uku aka yi garkuwa dasu amma yan bindigar sun saki mutum daya domin ya kai labari gida,” ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like