‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban kramar hukumar Yagba a jihar Kogin Najeriya, sun nemi a biya su naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

A ranar Asabar ‘yan bindigar suka sace Mr. Pius Kolawale bayan da suka bude wa motarsu wuta akan hanyarsa ta koma gida daga Ilorin.

Wannan hari ya yi sanadin mutuwar shugaban hukumar fansho na jihar Solomon Adebayo wanda suke tare da shi a lokacin.

Rahotanni daga Najeriya sun ce da yammacin jiya Lahadi ‘yan bindigar suka kira sakataren karamar hukumar ta Yagba da kuma wani daga cikin iyalan Kolawole.

Tun bayan aukuwar lamarin, rahotanni sun ce an baza jami’an tsaro a yankin da harin ya faru domin ganin an ceto shugaban hukumar Kolawole.

Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako guda, bayan da aka kai wani hari akan Sanata Clifford Ordia da ke wakiltar mazabar Edo Central a majalisar dokokin Najeriya a yankin jihar ta Kogi.

Yankuna da dama na jihar wacce ba ta da nisa da Abuja, babban birnin Najeriya, sun shiga kangin masu garkuwa da mutane.

Ko a watan Janairun bana, sai da wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan kasuwar kantin kwari 18 a yankin na jihar Kogi, a lokacin suna kan hanyarsu ta zuwa garin Aba domin sayo kayayyaki.

Amma an sako su daga baya, bayan da aka biya kudin fansa kamar yadda rahotanni suka nuna.