Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a jihar Katsina


Masu garkuwa da mutane sunyi garkuwa da sun yi garkuwa da wani mai rike da sarautar gargajiya a kauyen Zandam mai suna Babangida Lawal a karamar Jibia dake jihar.

Lamarin da yafaru a daren ranar Lahadi ya haɗa da wani sanannen dan kasuwa dake karamar hukumar mai suna Murtala Rabe da masu garkuwar shima suka yi awon gaba da shi.

Wani wanda ya sheda abinda ya faru kuma ya nemi a boye sunansa ya ce yan bindiga dauke da makamai sun farma garin inda suka fasa gidajen wasu masu fada aji dake garin suka kuma yi awon gaba da su.

“Wasu daga cikinmu da muka yi kokarin ceto su mun samu rauni sosai ya zuwa yanzu babu kudin fansar da aka dora akansu,”ya ce.

Har ila yau a kauyen Magarya mai makotaka da kauyen na Zandam yan bindigar sun sace wasu shanu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Katsina,SP Gambo Isa ya fadawa yan jarida ” Ƴansanda na sane da batun garkuwar kuma suna kokarin kubutar da su.”


Like it? Share with your friends!

-1
79 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like