‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto a Kaduna


Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga sun yi garkuwa da Elisha Noma, fasto a Cocin Nagarta Baptist dake Angwan Makiri a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Yan bindigar da yawansu ya kai 20 sun sace faston tare da dansa da misalin karfe 1:30 na daren ranar Laraba.

Sun kutsa kai da karfin tuwo cikin gidan faston inda suka sace kayayyaki.

Daga bisani yan bindigar sun sako dan nasa mai suna Emmanuel.

A cewar Emmanuel sun yi barazanar kashe mahaifinsa idan suka gaza biyan kudin fansa cikin kwanaki biyar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like