Yan bindiga sun yi garkuwa da wani alkali


Abdul Dogo, alkalin babbar kotun tarayya dake Akure ya fada hannun masu garkuwa da mutane.

An yi garkuwa da Dogo tare da direbansa a wajejen Ibilo/Isua Akoko wani gari dake kan iyakar jihohin Ondo da Edo akan hanyarsa ta dawowa daga Abuja.

Wani jami’in kotun wanda baya so a bayyana sunansa, ya ce masu garkuwar sun tuntubi iyalan alkalin inda suka bukaci a biya miliyan 50 a matsayin kudin fansa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ondo,Femi Joseph ya tabbatar da yin garkuwa da alkalin amma yace bashi da masaniya game da tuntubar iyalansa kan kudin fansa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like