Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane uku a Kano


Wasu gungun yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku akan hanyar dajin Falgore dake Kano.

Yan bindiga sun kafa shingen ne akan titin Kano zuwa Doguwa da ya ratsa ta cikin dajin.

Wani mutum mai suna, Ado Musa da ya sheda faruwar lamarin ya fadawa gidan rediyon Freedom dake Kano cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 07:00 na safiyar ranar Litinin.

Ya kara da cewa lamarin ya rutsa da matafiya da dama ciki har da, Mukhtar Abdulmumin kwamandan Hisbah na karamar hukumar wanda ya samu rauni


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like