Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 9


Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya su 9 da ake zargi har da masu aikin hidamtawa kasa NYSC da suke tafiya cikin wata motar haya a jihar Rivers.

Motar mai rijistar namba BWR 362 XC an yi mata kwanton bauna a wajen yankin Egele da ya hada jihar ta Rivers da kuma Bayelsa.

Amma fasinjoji hudu sun samu nasarar tserewa kafin a sace su.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Nnamdi Omoni ya ce wadanda suka kubuta rundunar ce ta samu nasarar kubutar da su.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ya ce babu yan hidimar kasa cikin matafiyan da aka yi garkuwa da su.


Like it? Share with your friends!

1
56 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like