Yan bindiga sun yi garkuwa da mai bawa gwamnan Nasarawa shawara


An yi garkuwa da Mr. John Waje mai bawa gwamnan jihar Nasarawa shawara kan harkokin kananan hukumomi, masarautu da kuma cigaban al’umma.

Wasu yan bindiga ne suka sace shi ranar Asabar da ta wuce da daddare a gidansa dake garin Dari a karamar hukumar Kokona ta jihar.

Wani da ya sheda faruwar lamarin ya ce mai bawa gwamnan shawara na tare ne da abokansa lokacin da masu garkuwar suka yi dirar mikiya a gidansa suna harbin kan me uwa da wabi domin tsorata mutane.

Shedar ya kara da cewa a yamutsin da ya biyo bayan harbin matasan garin sun samu nasarar kama daya daga cikin masu garkuwar.

Kawo yanzu masu garkuwar basu tuntubi iyalan mai bayar da shawarar ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like