Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 28 a jihar Ondo


Jumullar matafiya 28 ne dake cikin motocin haya ake zargin wasu yan bindiga sun yi garkuwa da su akan hanyar Ado-Akure dake jihar Ondo.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun dakawa matafiyan wawa a dai-dai lokacin da suke tafiya a wani sashe na titin da ya yi matukar lalacewa.

A tabakin mazauna yankin fasinjojin na cikin motoci biyu daya mai cin mutane 18 da kuma dayar dake dauke da mutane 9 har direba.

Wani bidiyon faruwar lamarin da aka wallafa a shafin Twitter ya nuna yadda mazauna yankin ke nuna bacin ransu kan rashin kyawun hanyar abin da suke ganin ya saukakawa masu garkuwar wajen gudanar da ta’asar ta su.

Lamarin na faruwa ne sa’o’i kadan bayan da gwamnonin yankin kudu maso yawa suka fara gudanar da wani taro da masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro kan yadda ayyukan masu garkuwa da mutane ke kara yawa a yankin.


Like it? Share with your friends!

1
73 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like