Yan bindiga sun yi garkuwa da alkalin kotun daukaka kara


Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Laraba sun yi garkuwa da alkalin kotun daukaka kara ta tarayya reshen Benin, mai shari’a Chioma Nwosu a Benin babban birnin jihar Edo.

Lamarin ya faru ne akan titin Benin-Agbor kusa da Cocin Christ Chosen.

Yan bindigar sun kashe dogarinta,insifecta A.I Momoh yayin da direbanta ya samu munanan raunuka.

Yan bindigar da yawansu ya kai hudu a cikin motarsu kirar Toyota Voltron sun biyo sahunta ne daga wurin hutawa na Ramat Park suka kuma samu nasarar tsare motar a wurin cocin inda anan take suka budewa dogarin nata wuta.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar wannan lamarin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like