Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Dalibai 6 A Wata Makaranta Dake Jihar Legas Wasu yan bindiga da ake zargin yan ta’adda ne sun kai hari wata makaranta dake jihar Legas inda sukayi awon gaba da dalibai shida.

Akwai rahotannin dake cewa a cikin wadanda aka sace akwai Shugaban karamar sakandire da kuma na babbar sakandiren makarantar. 

Wannan ne dai karo na biyuda yan bindigar suke kai hari akan Makarantar a cikin watanni biyar.

 Jaridar The Nation ta rawaito cewa tuni aka tura jami’an tsaro domin su duba dajin dake kusa da makarantar ko za’a samu nasarar ceto daliban. 

Yan bindigar dai sun aikewa hukumomin makarantar cewa zasu kawo hari makarantar.

A harin farko da suka kai makarantar yan bindigar sunje makarantar sanye da kayan sojoji inda suka yi awon gaba da dalibai da malamai. 

Tuni tawagar yan sanda karkashin jagorancin kwamishinan yan sandan jihar, Fatai Owoseni, suka kai ziyara makarantar. 

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like