Wani mazauni kauyen ne ya shaidawa Muryar Amurka aukuwan lamarin da alkawarin cewa ba za a ambaci sunansaba.

A cewarsa, an kona masu gidaje lamarin da ya sa suka tsere daji da su da iyalansu, yana mai cewa ba su samu wnai dauki daga jami’an tsaro ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Sulaiman Yaya Guroje ya tabbatar mana da aukuwan lamarin amma ya ce sun samu izini daga kwamishinan ‘yan sanda kuma tuni rundunar sojojin jihar ta kai taimako.

Wani masanin tsaro kuma shugaban kungiyan stofin sojoji na arewacin Nijeriya Malan Bashir Baba Yola ya ce rashin aiki ne yakan jefa al’umma ciki irin wannan mumunan hali.

A ‘yan kwanakin nan wasu yankunan jihar ta Adamawa na shiga kangin mahara, wadanda kan far wa kauyuka su halaka mutane.

Saurari rahoto cikin sauti daga Salisu Muhammed Garba: