‘Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Garin Dan Sadau A Zamfara
Sai dai a yayin harin, jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ‘yan sa kai a garin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan inda suka sami nasarar dakile harin suka kora maharan inda suka fito.

Da misalin karfe 11 da minti 54 ne aka fara jin harbin bindiga a garin na Dan Sadau inda mutane suka shiga rudani tare da neman yadda za su tsira da ransu lamarin da jami’an tsaro suka shawo kan sa ta hanyar yin musayar wuta da bata-garin.

Ya zuwa wannan lokacin dai kura ta lafa a garin inda mutane suka dan fara fitowa dan gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda suka saba amma dai ana cikin zaman zullumi kan abun da ka iya je ya dawo kamar yadda wakilinmu a jihar Zamfara ya shaida mana.

A cikin daren ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wane ne ba suka aukawa garin Dan Sadau dake jihar Zamfara inda suka kashe wasu mutane hudu tare da yin awun gaba da wasu mutum 13 ciki har da matan aure hudu.

A cikin mutane hudu da suka rasa ransu dai, uku daga cikin su raunin harbin bindiga ya yi sanadiyyara mutuwarsu inda ‘yan bindigan suka yi wa dayan matashin yankan rago.

‘Yan garin dai na ci gaba da mika kokensu ga gwamnati ta kawo mu su dauki kan yanayin da suka sami kan su ciki na rashin tsaro.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto gwannati ba ta ce uffan ba kan wannan hará na baya-bayan nan.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg