Yan bindiga sun sace yan uwan dan majalisar tarayya a Katsina


Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi dirar mikiya a gidan dan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar kananan hukumomin Kankia/Ingawa, Abubakar Yahaya Kusada inda suka yi awon gaba da yan uwansa biyu.

Yan bindigar sun sace yan uwansa biyu da suka hada da Sulaiman Musa da Talatu Musa inda suka bar mutum na uku a cikin jini face-face.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare a kauyen Gidan Mutum dake karamar hukumar Kusada ta jihar Katsina.

A zantawar da ya yi da jaridar Sahelian Times Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina,Gambo Isa ya ce kawo yanzu basu samu labarin rahoton faruwar lamarin ba

Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro inda koda a makon da ya wuce sai da aka sace wasu manyan jami’an yansanda su 9.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like