Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Plataeu


Yan bindiga sun yi garkuwa da David Dongbam basaraken gargajiya mai daraja ta biyu na masarautar Dorock dake ƙaramar hukumar Shandam ta jihar Plataeu.

Terna Tyopev, mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce anyi garkuwa da Dangbam a gidansa dake Shandam ranar Litinin da daddare.

Tyopev ya fadawa NAN, “jiya da misalin karfe 10 na dare mun samu bayanai dake cewa wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun yi dirar mikiya a gidan Longdorock, Mista David Dongbam basaraken gargajiya mai daraja ta daya na masarautar Dorock dake karamar hukumar Shandam,ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“Bayan mun samu labarin mun kafa wata tawaga da zata gudanar da bincike tdake aiki ba kakkautawa dan kubutar da basaraken gargajiyar ba tare da ko kwarzane ba.”

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar ta Plataeu ya ce rundunar zata cigaba da sanar da jama’a irin cigaban da ake samu a aikin kubutar da basaraken.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like