Yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na Nasarawa


Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun sace shugaban jam’iyar PDP na jihar Nasarawa,Mr Philip Tatari Shekwo.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa, Mr Emmanuel Bola Longe ya fadawa manema labarai cewa yan bindiga masu yawan gaske sun yi dirar mikiya a gidan shugaban jam’iyar dake kusa da cocin Dunamis a unguwar Bukan Sidi dake Lafiya a jiya Juma’a da misalin karfe 11 na dare inda suka dauke shi ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Ya kara da cewa tuni jami’an tsaro suka bazama ya zuwa dazuzzuka dake sassan jihar domin tabbatar da an sako shugaban jam’iyyar.

Batun garkuwa da mutane abu ne da ya zama ruwan dare a jihohin arewacin Najeriya.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like