‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar ABU Zaria Guda 17 A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja


‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria su 17 a babban titin Kaduna zuwa Abuja.

The Abusites, jaridar jami’ar ne ya ruwaito afkuwar lamarin a ranar Litinin.

A cewar rahoton, waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin daliban aji 3 ne a tsangayar koyar harshen Faransanci da ke hanyarsu na zuwa Legas don hallartar shirin koyon harshen Faransanci a Nigerian French Language Village, NFL.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like