Yan bindiga sun kashe yan bijilante 50 a jihar Zamfara


Barayi masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun kashe yan Civilian JTF sama da mutane 50.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Sunusi Rikiji shine ya bayyana haka ranar Juma’a lokacin da yakai ziyarar ta’aziya masarautar kauran Namoda.

Kakakin majalisar ya alakanta kashe mutanen da arangamar da aka yi tsakanin yan Civilian JTF da kuma barayin a wani kauye dake karamar hukumar Kauran Namoda.

Rikiji wanda ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin jihar ya koka kan tabarbarewar yanayin tsaro a jihar.

Har ila yau Rikiji ya ce tuni gwamnatin jihar ta tattara sunayen mutanen da abin ya shafa domin tallafawa iyalansu.


Like it? Share with your friends!

-4
72 shares, -4 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like