Yan bindiga sun kashe shanun fulani makiyaya a jihar Plateau


Fulani makiyaya sun yi zargin wasu yan bindiga a jihar Filato sun kashe shanu 80 tare da sace wasu 32 a kusa da kwalejin aikin akanta dake Kwall karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Plateau ya turawa jaridar Daily Trust sakon Imail mai dauke da hotunan matattun shanun inda ya fadawa yan jaridu cewa shanu 81 aka harbe aka kuma sassara wasu da adda yayin da aka sace 32 kana aka dauki 48 da suka jikkata zuwa mayanka don gudun asara.

Abdullahi ya ce tuni suka sanar da rundunar samar da tsaro dake jihar da akewa lakabi da Operation Safe Haven da kuma kwamishinan yansandan jihar,Isaac Akinmoyede kuma duk sun tura wakilai ya zuwa wurin da lamarin yafaru.

Anasa bangaren shugaban kungiyar matasan fulani ta Najeriya, Sa’idu Maikano ya ce ankai harin ne da gayya domin harzuka fulani makiyaya inda yace yayi mamaki da har yanzu gwamnatin jihar ta gaza fitar da wata sanarwa dake alla wadai da faruwar lamarin.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like