Yan bindiga sun kashe mutum guda tare da sace yayan shugaban karama hukuma a Katsina


Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutum guda tare da sace ‘ya’yan kantoman riko na karamar hukumar Matazu.

Lamarin ya zama wani babban nakasu ga yunkurin gwamnan jihar Aminu Bello Masari na samar da zaman lafiya ta hanyar yin sulhu da yan bindiga dake dauke da makamai a kananan hukumomi 8 na jihar.

Karamar hukumar Matazu na daya daga cikin ƙananan hukumomin jihar da harin na yan bindiga bai shafa ba.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,SP Gambo Isa ya fadawa manema labarai a Katsina cewa lamarin ya faru da tsakar daren ranar Laraba.

Ya bayyana mutumin da aka kashe a matsayin jami’in tsaro a gidan shugaban karamar hukumar, Alhaji Kabir Matazu.

Isah ya ce yan bindigar bayan sun kashe mai gadin sai suka yi a won gaba da yaran.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like