Yan bindiga sun kashe mutane uku a Katsina


Mutane uku aka rawaito an kashe tare da jikkata wasu uku a wani hari da yan bindiga suka kai kan kauyen Marar Zamfarawa dake karamar hukumar Dan Musa a jihar Katsina.

Yan bindigar da suka isa kauyen da kafa sun kaddamar da harin ne da tsakar daren ranar Juma’a.

Mazauna kauyen da kuma jami’an tsaro sun fuskanci su a kokarin da su kayi na dakile harin.

A cewar mazauna kauyen waɗanda aka kashe sun hada da Aminu Yusuf, Lawal Akushi da Mansir Danliti wadanda kuma suka jikkata sun hada da Rabi’u Mala, Shamsu da kuma Sharhabilu da ake yi musu magani a babban asibitin Danmusa.

An binne wadanda sukt mutu ranar Asabar da safe bayane da aka yi musu jana’iza.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like