Yan bindiga sun kashe mutane 17 a sabon harin da suka kai Katsina


Akalla mutane 17 aka kashe da dama kuma suka samu munanan raunuka da ka iya sanadiyyar mutuwarsu bayan wani hari da yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka uku a jihar Katsina.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutane hudu aka kashe a kauyen Tsayau dake karamar hukumar Jibia, 11 a kauyen Dantakuri, 2 a kauyen Birza dukkansu a karamar hukumar Danmusa.

Hare-haren da aka kai ranar Lahadi daga karfe 7 zuwa 12 na dare a cewar mazauna ƙauyukan sai kuma garkuwa da mutane ta biyo baya tare da lalata dukiya da kuma sace dabbobi masu yawa.

Wasu shedun gani da ido sun bayyana cewa mutanen kauyen na kididdige asarar da suka yi da kuma gano wadanda aka yi garkuwa da su.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa mutanen kauyen Tsayau sun dauke gawarwakin ya zuwa fadar sarkin Katsina,Abdulmuminu Kabir Usman domin yin zanga-zangar kisan da aka yi.

Tuni rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar harin da aka kai kan kauyen Tsayau ta bakin mai magana da yawunta, ASP Anas Gezawa.


Like it? Share with your friends!

1
85 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like