Yan bindiga sun kashe manoman albasa 10 a Zamfara


Wasu yan bindiga a jihar Zamfara da ake kyautata zaton barayine sun harbe wasu manoman albasa 10 a kauyen Kursasa dake gundumar Kwari a karamar hukumar Shinkafi dake jihar.

Gundumar Kware ta dade tana fuskantar jerin hare-hare cikin makonni shida da suka gabata daga wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba.

Tsakanin watannin Faburairu da Maris a ƙalla mutane 62 aka kashe a wasu munanan farmaki da aka kai gundumar.

Mazauna kauyen sun bayyana cewa maharan sun isa akan babura inda suka bude huta kan manoman dake aiki a gonakinsu. manoman sun yi kokarin tserewa amma suka gaza yin nasara.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,ya tabbatar da faruwar harin amma ya ce tuni aka tura jami’an tsaro ya zuwa yankin domin dawo da doka da oda.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like