Yan bindiga sun kai hari gidan wani babban jami’in soja a jihar Benue


Yan bindiga a ranar Litinin sun kai hari gidan, Manjo Janar John Malu dake kauyen Tsai Adoo a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

Amma mai da martanin gaggawa da jami’an tsaron dake kare lafiyarsa suka yi shi ya jawo aka samu nasarar dakile harin.

Manjo Janar John Malu kani ne ga tsohon babban hafsan sojojin kasarnan, Victor Malu.

An rawaito cewa yan bindigar da ba a san ko suwaye ba sun dirarwa gidan banban sojan inda suka shiga harbi ba kakkautawa kafin sojoji su fatattake su.

Malu ya ziyarci gidansa dake mahaifarsa lokacin da lamarin ya faru da safiyar ranar Litinin.

Kwamandan bataliya ta 72 dakarun sojan Najeriya, laftanar Kanal, Sulaiman Muhammad ya tabbatarwa da manema labarai dake makurdi cewa yan bindiga sun kai hari gidan Malu amma an samu nasarar fatattakar su.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like