Yan bindiga sun kai hari ofishin yansanda a jihar Edo


Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe babban baturen yansanda na ofishin yansanda dake Afuze, hedkwatar karamar hukumar Owan East dake jihar Edo.

Har ila yau yan bindigar sun kashe wasu jami’an yansanda hudu dake bakin aiki ciki har da wata yarsanda dake dauke da juna biyu.

Yan bindigar sun kuma kai hari ofishin hukumar zabe dake garin inda suka lalata kayayyakin zabe tare da kona motar ƴansanda dake bayar da tsaro a ofishin.

Jami’an da aka kashe a harin sun hada da babban baturen yansandan, Tosimani Ojo Justina Aghomon wata mace mai juna biyu , Sado Isaac da kuma Glory Da.

Wani sheda mai suna, Godwin Ikpekhia ya fadawa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa lamarin yafaru ne ranar Talata da misalin karfe 8 na dare lokacin da sauran jami’an suka fita sintiri.

“Kawai dai munji karar harbin bindiga babu wanda yasan hakikanin abinda ya faru har sai da safiyar ranar Laraba,” ya ce.

Kwamishinan yansandan jihar, Muhammad Dammallan wanda yaje wurin da abin ya faru yace tuni aka fara bincike domin gano wadanda ke da hannu a harin

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like