Yan bindiga sun harbe yan sanda biyu a Taraba


Wasu yan bindiga da kawo yanzu ba a san ko suwaye ba sun kashe yan sanda biyu a karamar hukumar Karim Lamido dake jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa an harbe yan sandan ne da misalin karfe 7 na daren ranar Litinin a kusa da mahadar Jen dake kan titin Karim Lamido bayan da motar sintirinsu ta lalace.

Mamatan na tsaka da gyaran motar ne lokacin da yan bindigar suka nufo su akan babur inda suka bude musu wuta suka kashe biyu nan take.

Yan bindigar sun kuma samu nasarar yin awon gaba da bindigogin jami’an yan sandan biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Taraba, ASP David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 6

You may also like