Yan bindiga sun harbe tsohon babban hafsan tsaron Najeriya,Alex Badeh


Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe tsohon babban hafsan sojan Najeriya, Alex Badeh.

Ƴan bindigar sun harbe shi har lahira a wani harin kwanton bauna da suka kai masa akan hanyar Abuja zuwa Keffi.

Badeh ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da ya samu harin lokacin da yake kan dawowa daga gonarsa.

Mai magana da yawun rundunar sojan saman Najeriya, Ibikunle Daramola ya tabbatar da mutuwar cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sakon ya kuma taya iyalansa dama al’ummar kasa baki daya alhinin wannan babbar rashi da aka yi.

Badeh ya kasance shugaban rundunar sojan saman Najeriya daga shekarar 2012 ya zuwa 2014 inda aka daga likkafarsa ya zuwa babban hafsan sojan Najeriya.

Hukumar Efcc ta gurfanar da marigayin a gaban kotu a watan Fabrairu na shekarar 2016 inda take tuhumarsa da karkatarwa da kuma halarta kudaden haram zarge-zargen da ya musalta aikatawa.

Badeh ya fito ne daga garin Vimtim na karamar hukumar Mubi ta jihar Adamawa.


Like it? Share with your friends!

-1
88 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like