Yan bindiga sun fatattaki mazauna kauyuka 16 daga gidajensu a jihar Kaduna


Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka 16 dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a ranar Lahadi.

Har ila yau rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kashe yan bijilante uku da suka shiga cikin daji domin fafatawa da su ya yin da wasu da dama ba a san inda suka shiga ba.

Mazauna kauyukan da aka raba da muhallinsu da yawa daga cikinsu mata ne da kananan yara da kuma tsofaffi, sun samu mafaka a makarantar firamare ta Birnin Yero dake kan hanyar Zariya zuwa Kaduna.

Wakilin jaridar Daily Trust da ya ziyarci makarantar ya rawaito cewa an jibge jami’an tsaro domin gudun karyewar doka da oda.

Dagacin kauyen Anguwar Gide,Malam Jibril Abdullahi ya ce yan bindigar sun yi dirar mikiya a kauyukan da yammacin ranar Lahadi inda suka umarce su da su fice daga yankin.


Like it? Share with your friends!

-1
91 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like