Yan bindiga sun bude wuta kan ayarin motocin gwamnan Borno


Ayarin motocin gwamna jihar Borno,Babagana Umara Zulum ya fuskanci hari daga wasu yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne a ranar Laraba a garin Baga dake jihar.

Wasu majiyoyi dake cikin jami’an tsaro sun bayyana cewa gwamnan na kan hanyarsa ne ta zuwa sansanin yan gudun hijira dake yankin na arewacin jihar lokacin da lamarin ya faru.

“Gwamnan yaje Kukawa kuma akan hanyarsa ta zuwa Baga an kai wa ayarin motocinsa hari. babu wanda aka jikkata,” a cewar majiyar.

Kawo yanzu kungiyar ta Boko Haram bata fito fili ba ta dauki alhakin kai harin.

Har ya zuwa karfe 09:10 na dare gwamnan bai koma birnin Maiduguri ba.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 3

Your email address will not be published.

You may also like