Yan bangar siyasa sun kashe dan majalisar wakilai daga Oyo


Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan bangar siyasa ne sun harbe,Temitope Olatoye dan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar mazabar Lagelu/Akinyele dake jihar Oyo.

Wasu majiyoyi sun sheda cewa yan bindigar sun harbe Olatoye ne a ƙauye Elesu dake karamar hukumar Lagelu ta jihar.

An dai garzaya da shi asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan.

Bayan da likitoci suka gaza ceto rayuwarsa a karshe ya mutu sakamakon harbin da aka yi masa a ido.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like