Yan Afrika ta kudu dauke da makamai sun fara zanga-zangar neman baki su bar kasar


Wani sabon rikici na shirin barkewa a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu ya yin da masu zanga-zanga dauke da makamai suka sake fitowa kan tituna suka bukaci baki yan kasar waje da su koma inda suka fito.

A cewar jaridar Swetan Live ta kasar, masu zanga-zanga dake dauke da muggan makamai sun fito inda suke jiran jawabi daga Mangosuthu Buthelezi,wani dan siyasa kuma jagora a kabilar Zulu.

Hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan hari kan baki yan kasashen waje ya jawo martani mai zafi daga kasashe da dama a nahiyar.

Najeriya,Ruwanda da Malawi sun kauracewa taron tattalin arzikin duniya da aka gudanar a kasar Afrika ta Kudu ya yin da kasar Zambia ta soke yin wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafar kasar ta Bafana Bafana.

A harin ramuwar gayya a Najeriya an kai wa wasu kamfanoni dake da alaka da kasar ta Afrika ta kudu farmaki.


Like it? Share with your friends!

-1
100 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like