Yakin Neman Zabe: An ci kasuwar jar hula a jihar Kano


Mun samu rahoton cewa, masu sayar da jar Tagiya a jiya Lahadi cikin birnin Kano sun dara wajen cin kasuwar su a harabar filin wasanni na Sani Abacha yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar.

Rahotannin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito sun bayyana cewa, jihar Kano ta cika ta batse a jiya Lahadi yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, sanya jar Tagiya musamman a jihar Kano da wasu jihohin Arewa manuniya ce ta akidar magoya bayan kungiyar Kwankwasiyya da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya assasa.

Wani daga cikin masu sana’ar sayar da jar hula, Mallam Ibrahim Maihula, yayin ganawar sa da manema labarai ya bayyana cewa, a yau cike yake da farin ciki domin kuwa tun gabanin rana ta yi zawwali ya sayar da fiye da hulana 250 da ya kasa a harabar filin wasanni na Sani Abacha.

Kazalika, wani dan kasuwar na daban, Umar Lawan, da ya taso tun daga karamar hukumar Gwarzo domin halartar taron yakin zaben Atiku, ya ce ya samu nasarar sayar da huluna fiye da 300 da ya kasa a jiya cikin birnin Kanon Dabo.

A Jiya Lahadi dai jhar Kano ta cika ta batse yayin da al’umma suka yi tururuwa tamkar kudan zuma domin halartar taron yakin zaben Atiku wanda masu sharhi suka misalta a matsayin gagarumin taron siyasa da ba a taba samun makamancin sa fadin Najeriya.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like