Yakin Da Rashawa Ya Zama Wasan Kwaikwayo A Gwamnatin Buhari – Hajiya Naja’atu


Wata fitacciyar ‘yar siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Hajiya Naja’atu Mohammed ta ce babu gaskiya cikin yaki da gwamnatinsu ke yi da cin hanci da rashawa.

Hajiya Naja’atu Muhammad daya daga cikin wadanda suka rika tallata Muhammadu Buhari tun a zaben 2003 ta shaida wa BBC cewa ba wani yaki da rashawa da gwamnatinsu ke yi

Tace “Mutum nawa aka kama, wasan kwaikwayo ne kawai ake yi,” in ji ta.

Sai dai kuma a cikin jawabinsa na gabatar da kasafin kudi a zauren majalisa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori a yaki da cin hanci da rashawa, kuma nan ba da jimawa ba ‘yan kasar za su ci moriyar kudaden da aka kwato.

Hajiya Naja’atu Muhammad ‘yar siyasa daga jihar Kano ta yi tsokaci ne game da wasu jerin bidiyon da aka wallafa da ke zargin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudaden da aka ce cin hanci ne daga hannun ‘yan kwangila.

Ta kalubalanci gwamnatin tasu a kan rashin gudanar da bincike kan lamarin, duk da ikirarin da ta ke yi cewa tana yaki da rashawa.

“Idan zargi ne, me ya sa ba a yi bincike ba? Ai, idan ba a yi zargi ba, ba za a yi bincike ba. Idan ba a yi bincike ba, ai ba za a gano gaskiya ba.”

Ta ce a iyakar saninta, kotu ba ta isa ta hana ‘yan sanda bincike ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like