Yahaya Bello ya yi watsin kudi a Abuja


Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi ya jawo cinkoson ababen hawa a Gwagwalada dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja ranar Laraba bayan da ya rika watsawa mutane kudi.

A cewar jaridar Daily Trust gwamnan wanda yake cikin ayarin jerin gwanon motocin sa akan hanyarsa ta zuwa Lokoja daga Abuja ya tsaya a mahadar Madam Mercy inda ya fito da rafar kudi guda uku ta yan ₦500 ya rika watsawa mutane masu wucewa.

Rahotanni sun nuna cewa an samu tsaikon ababen hawa na tsawon mintuna 10 inda ya rage gilashin motarsa tare da daga yatsu 8 dake nuna alamar 4+4.

Wasu masu wucewa, masu sayar da kayayyaki da kuma yan acaba sun kauracewa wuraren sana’arsu inda suka shiga wawar kudin.


Like it? Share with your friends!

1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like