Yahaya Bello ya sanar da aniyarsa ta neman zango na biyu


Gwamnan jihar Kogi,Yahaya Bello ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takara a zaɓen gwamnan jihar da za gudanar a karshen shekara.

A cewar Muhammad Onogwu jami’in yada labaran gwamnan, Bello ya bayyana aniyar tasa ne a wurin bikin kaddamar da hukumar dake kula da majalisar dokokin jihar,a Lokoja.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne bayan tuntubar shugabancin jam’iyyar APC a matakin jiha da kuma kasa baki daya.

Ya kara da cewa ya zama wajibi ya bayyana aniyarsa ta yin takara bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin gudanar da zaben gwamnan jihar.

Hukumar zabe ta INEC ta sanya ranar 2 ga watan Nuwamba a matsayin ranar gudanar da zaben gwamnan jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like