Yahaya Bello: Karin wasu gwamnonin PDP na nan tafe cikin APC


Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce gwamnoni da dama na jam’iyar PDP na shirin komawa jam’iyar APC.

Bello wanda ya kasance bako a cikin shirin Siyasa a Yau na gidan talabijin na Channels ya yi tsokaci kan sauya shekar gwamnan jihar Ebonyi,Dave Umahi zuwa jam’iyar APC.

“Umahi yana tare da mu, sauran suna zuwa. Sauran gwamnonin tuni suke kwankwasa kofa. Suna kan hanyarsu.Zamu rika karbarsu daya bayan ɗaya,” ya fada.

Bello ya ce APC ta bada himma wajen fitar da dan takara a zaɓen 2023 da zai hada kan kasa da kuma karɓuwa ga kowa da kowa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like