Yadda Wani Dan Kasar Sin Ya  Gurgunta Ma’aikacinsa Dan Najeriya 


William Ekanem, ma’aikacine  a kamfanin samar da kayayyakin gado da kujeru na Bedmate dake jihar Ogun,  ya samu matsala a lakarsa bayan da maigidansa dan kasar Sin wato China  da ake kira Masta Wan ya dakeshi.

Wan wanda akace ya kware a salon fadan nan na mutanen Sin da ake kira Kung Fu. Ya bukaci yaga buhun shinkafa da Ekanem ya siya  a wurin wata mata da ake kira madam Iya Melo dake sai da kayan abinci a harabar kamfanin. 

 Ekanem, ya kalubalanci,Wan kan yadda yake shiga harkokinsa. 

Bayan ya duba abin da ke cikin buhun da karfin tsiya, Ekanem yace yayin da ya juya zai tafi sai Wan ya doke shi a baya dukan da yasa nan take yayi juyi ya fadi a kasa.

Mutumin da ake zargi Masta Wan yabi Ekanem ya take shi da kafa kafin sauran ma’aikatan dake kamfanin su ceceshi daga hannunsa. 

 Tun bayan da abin yafaru a watan Afirilu,Ekanem baya iya tafiya dakyu ko kuma ya tsaya a tsaye.

Ekanem yace duk da sunkai rahoton faruwar lamarin ga caji ofis din yan sanda,sun zargi yan sandan da karbar naira dubu hamsin a matsayin na goro daga kamfanin domin a rufe maganar. 

 

Comments 0

Your email address will not be published.

Yadda Wani Dan Kasar Sin Ya  Gurgunta Ma’aikacinsa Dan Najeriya 

log in

reset password

Back to
log in