Wata yarinya ‘Yar Shekara 15 dalibar makarantar mata dake Dapchi a Jahar Yobe a Najeriya ta bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya a harin da ‘Yan Kungiyar Boko Haram suka kai makarantar tasu ranar Litinin data gabata inda suka kwashe daliban mata sama da 100 suke garkuwa dasu

Da take zantawa da jaridar The Nation, Yarinyar Mai suna Amina Malam Usman tace:

“Lokacin da ‘Yayan Kungiyar ta Boko Haram suka zo makarantarmu mun zaci sojoji ne, saboda sunyi shiga irinta sojoji. Sai muka sheka aguje muka ranta ana kare, sai daya daga cikinsu ya kiramu. Sai wani daga cikinsu yace inzo kusada motar.

Lokacin da nazo kusada motar, sai daya daga cikinsu ya fara mini dariya, na kara matsawa kusada su, ina zaton sojoji ne.

Daga sai jikina Ya bani cewar wadannan ba sojoji bane, sai nayi kokarin shekawa aguje inda wani daga cikinsu yayi kokarin kamani saina subule masa amma ya samu ya janye hijabi na.

Sai nayi sauri na subule hijabin nabar masa na runtuma aguje. Nayi tsammanin na mutu.

Sai suka shiga dakunan kwananmu na dalibai, amma tuni wasu sun runtuma da guda cikin jeji. Nayi gudan fitar rai na akalla kilomita 5 inda na taradda wani kauyen Fulani da ake kira Miligiya na buya anan”

Lokacin da aka tambayi Amina ko zata iya tuna ko dalibai nawa ta gani a cikin motar wadanda suka zo yin garkuwa dasu sai tace:

” Gaskiya sunada yawa domin akalla wadanda nagani a cikin motar a lokacin zasu kai Kimanin 50″

Tace a lokacin ji tayi inama ace mala’ikan mutuwa Ya zare ranta a lokacin da ta fahimci cewar wadannan mutanen Yan kungiyar Boko Haram ne.

Tace ita a yanzu gaskiya batajin zata iya sake komawa wannnan makarantar tasu dake Dapchi

Fatan mu Allah ya bayyana su Amin summa Amin.