Yadda Muka Yi Rayuwa A Hannun Masu Garkuwa-Fasinjar Jirgin Kasa
Malam Muktar Shu’aibu daya daga cikin mutane biyar da ‘yan-bindiga su ka saki ranar Talata, ya ce sun yi fama da rashin lafiya da kuma zaman zullumi na rashin sanin makomar su a daji lokacin da su ke hannun ‘yan-bindigan.

A hirar shi da Muryar Amurka, Shu’aibu wanda aka samu yana zaune cikin ‘yan’uwan shi da masu zuwa don jajantawa, ya ce masara su ke ci safiya da rana sai kuma a daidaikun ranaku akan kawo musu shinkafa. Ya ce faifan bidiyon da aka nuna ‘yan-bindigan na dukan su gaskiya ne amma fushi su ka yi sakamakon hana ‘yan’uwan wadanda aka sacen zuwa dajin don karbo su.

Game da harbin Al’amin Muhammad kuwa malam Muktar Shu’aibu ya ce kuskure aka yi kuma yanzu ya na cikin wadanda aka sako ranar Talata. Ya ce har yanzu akwai mutane 34 a daji ba a sako su ba. Ya ce sau biyu ‘yan-bindigan na basu naira dubu goma-goma don su kashe . Ya kuma bayyana cewa, a gidan shugaban ‘yan-bindigan da ke cikin dajin su ke sayen abun da su ke sha’awa.

Saurari cikakkarkar hirar shi da Isa Lawal Ikara cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg