Yadda Jami’an Tsaro Suka Kubutar Da Mutum 77 Da Aka Tsare A Dakin Wata Mujami’a A Jihar Ondo
Hukumomin tsaro a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya, sun kama Pastocin Mujami’ar Whole Bible Believers Church, bayan da aka kubutar da mutum 77 da ake zargin garkuwa aka yi da su, a wani daki da ke karkashin ginin Cocin a karshen makon nan.

Rahotanni sun ce, wasu daga cikin mutanen sun kai tsawo wata shida, a tsare a cocin.

Wata matashiya ta fadawa jaridar Punch da ake wallafa a Najeriya cewa, “na yanke shawarar shiga Cocin ce saboda iyayena suna janye ni daga bin dokokin Allah, alhali ina so na shiga Aljanna.”

Hukumomin sun ce sun kai samame Cocin cene bayan da wasu iyaye suka kai korafi wajen hukuma.

‘Yan sanda sun ce sun kama pasto da wasu mambobin Cocin.

Saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal daga Ibadan:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg