Hukumar ta DSS ta yi Allah wadai da wasu kalamai da abin d ata kira wasu marasa kishin kasa ke yi da ka iya wargazar da zaman lafiya a kasar da kuma barazana ga dorewar gwamnatin kasar.

DSS dai ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da kakakinta, Peter Afunanya, ya rattabawa hannu a ranar Lahadi tana mai cewa, abu mafi ban tsoro shi ne kalaman da ba su dace da kuma wasu ayyukan malaman addini da tsaffin shugabannin siyasa wadanda ke yin kira da gwamnati ta sauka daga kan karagar mulki.

Haka kuma, hukumar DSS ta ce bai kamata a ce Mutanen da ake gani a matsayin jagorori masu kima na yin irin wadannan kalamai domin biyan bukatun kashin kansu ba.

Ta kara da cewa, duk da cewa, mulkin dimokradiyya ya bayar da ‘yancin fadin albarkacin baki, amma ba ta bayar da damar yin kalaman ganganci da ka iya jefa tsaron kasa cikin halin ha’ulai ba.

Daga karshe dai hukumar, ta na aiki tare da sauran hukumomin tsaron kasar don tabbatar da dorewa zaman lafiya da tsaro a cikin kasar.