Yadda Ake Auren Mut’ah Da Kananan Yara A Iraki’


Wani binciken kwakwaf da BBC ta yi kan auren mut’ah ta gano yadda wasu malamai ke gudanar da auren mut’ah da kananan yara a Iraki.

Binciken sirrin da BBC ta yi a daya daga cikin wuraren da malaman suke domin gudanar da irin wannan aure ta gano cewa malaman na daura auren mutu’a na takaitaccen lokaci, a wani lokacin ma har na zuwa sa’a daya ko kwana daya.

Wasu malaman ma na aurar da har mata ‘yan shekara tara domin a sadu da su.

Binciken ya gano cewa malaman na sa albarka ga yara wadanda ba su kai shekarun aure ba domin su zama amare na takaitaccen lokaci.

Auren mut’ah wani sashe ne na addini a mazhabar Shi’a da wasu daga ciki ke yi, inda ake aure na dan takaitaccen lokaci, ana kuma biyan matan da aka yi auren da su kudi kafin gudanar da auren.

Asali auren mut’ah ana yin shi ne idan mutum zai yi tafiya sai ya tafi da matar, amma a yanzu namiji da mace za su yi auren mut’ah su zauna a gari daya na dan wani lokaci.


Like it? Share with your friends!

2
64 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like