Ya Yi Mankas Da Barasa Ta Fada Masa Karya Ya Banke ‘Yan Makaranta Da Mota.


Lamarin Ya Faru Ne A Daidai Barikin Soji Na Bukavo Dake Kano.

Shaidun Gani Da Ido Sun Shaida mana Cewa Mutumin Wanda Yataho A Motarsa Kirar Jeep Ya Banke Yara ‘Yan Makarantar Sakandiren Mata Ta Barikin Sojoji (Army Day) Yayin Da Suke Kokarin Shiga Babur Din Adaidaita Sahu, Wanda Hakan Yayi Sanadiyar Karyewar Wasu, Wasu Kuma Suka Sami Munanan Raunuka. Bayan Ya Aikata Wannan Ta’asar Ne Yayi Yunkurin Tserewa, Saidai Mutanen Da Ke Wajen Sun Sami Nasarar Hanashi Guduwa, A Nan Ne Suka Gane Cewa Wannan Aikin Kamru Ne.

Daga Karshe Dai Jami’an Tsaro Sun Tafi Da Mutumin Da Kuma Wadan Suka Jikkata, Domin A Kaisu Asibiti.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like