Ya Babbake Kansa Da Wuta Saboda matarsa Ta Guje Shi.


Kamar yadda kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa Audu Jinjiri ya bayyana, shi dai wannan magidanci mai shekaru 40 da hahuwa; mai suna Abdullahi Ja’afaru ya tuttula wa kansa fetur daga bisani kuma ya kyasta wa kansa wuta. Al’amarin ya faru ne a jihar Jigawa. Mutumin sun samu saɓani ne da matarsa mai suna Halima har ma ta yi yaji.

Majiyarmu ta bayyana cewa, dukkan ƙoƙarin da Ja’afaru ya yi don ganin ya dawo da uwargidan tasa kuma uwar yaransa shidda amma abin ya ci tura. Wannan shi ne dalilin da ya sanya shi ya zuciya, har ya babbake kansa da wuta. Duk kuwa da cewa, yana da wata matar wacce ya auro bayan Haliman.

A lokacin Allah ya taimake shi akwai jami’an ‘ƴansanda a kusa, nan da nan suka garzayo don cetonsa. Daga nan aka miƙa shi izuwa asibiti don kula da lafiyarsa.

Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan labari, Jaafaru yana asibiti a cikin mawuyacin hali, amma har yanzu bakinsa bai daina ambaton sunan matarsa Halima ba. Duk kuwa da ita Amaryar tasa tana tare da shi a asibitin tana tattalinsa, tana kula da shi sosai.


Like it? Share with your friends!

-1
105 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like